‘Yan sandan jihar Kebbi sun kama manyan motoci maƙare da tabar wiwi

0
245

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama manyan motoci guda biyu maƙare da ƙullin tabar wiwi da ba a taɓa kama irinsa ba a tarihin tsaro a jihar Kebbi.

A mota ta farko mai lamba IT 21520 LA, Lagos, ‘yan sanda sun kama surkin ƙullin wiwi guda 4,927 da aka ƙiyasta kuɗinsa ya kai fiye da Naira miliyan ɗari uku.

‘Yan sanda sun kama mutane uku masu suna Emmanuel Chukwuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Banden a jihar Abia, da Kanta Bisa ɗan ƙaramar hukumar Asaka a ƙasar Ghana, tare da Ishola Adeyemi, ɗan Unguwar Alufon, a ƙaramar hukumar Akure na jihar Ondo dangane da kayayyakin.

Kazalika ‘yan sanda sun sake kama wata motar mai lamba IT 21608 LA, Lagos, maƙare da surkin ƙullin tabar wiwi guda 4,906. ‘Yan sanda sun kama wani mai suna Abdulrazak Agboola, ɗan asalin Unguwar Yana Ajiya a birnin Ibadan, ɗauke da kayayyakin a cikin babbar motar.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NDLEA ta kama buhunan tabar wiwi 116 a Kano

An ƙiyasta cewa, jimillar ƙiyasin kuɗin surkin tabar wiwi da ‘yan sanda suka kama ya zarce naira miliyan ɗari shida.

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa an yi hayan direbobin motocin ne daga ƙasar Ghana domin su kawo tabar wiwi a kan kuɗi Naira 200,000 a mota ta farko yayin da aka yi alƙawarin biyan Naira 400,000 ga direban mota na biyu.

‘Yan sanda sun kuma kama albarushi Cartridges katon 30 wanda ke ɗauke da kwali goma a kowanne kuma akwai kwara 25 a ciki.

Leave a Reply