‘Yan sanda sun ƙwato shanu 77 da aka sace a Filato

0
247

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta gano wasu shanu 77 da ake zargin an sace su a unguwar kamfanin Zurak da ke ƙaramar hukumar Wase a jihar Filato.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Alfred Alabo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Jos.

Mista Alabo ya ce shanun da aka sace a ranar 11 ga watan Satumba mallakin wani Idris Yunusa ne ɗan unguwar Gajin Duguri a ƙaramar hukumar Alƙaleri ta jihar Bauchi.

“A ranar 19 ga watan Satumba, mun samu sahihan bayanai a sashinmu na Bashar cewa wasu miyagu sun sace wasu adadin shanu na wani Alhaji Idris Yunusa, Galadiman Yuli Duguri.

“A cewar rahoton na sirri, an sace shanun ne daga hannun wani makiyayi a lokacin da suke kiwo, yayin da suka nufi dajin Odare a ƙauyen Kampani Zurak na ƙaramar hukumar Wase.

“Bayan samun labarin, jami’in ‘yan sanda na Bashar (DPO) a Bashar ya jagoranci tawagar jami’an tsaro tare da jami’an tsaron gida da mafarauta, suka kama waɗanda ake zargin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kwato bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu a Kano

“Lokacin da suka ga jami’an tsaro, waɗanda ake zargin sun shiga cikin dazuzzukan da ke kusa.

Sai dai an ƙwato shanu 77 aka miƙa wa mai shi,” inji shi. Mista Alabo ya ce rundunar ta ƙara zage damtse wajen cafke waɗanda ake zargin tare da fuskantar fushin doka.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Julius Alawari, ya baiwa mutanen jihar tabbacin cewa rundunar tana ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyi.

Mista Alawari ya buƙaci mazauna yankin da su kula da harkokin tsaro kuma su kai rahoto ga jami’an tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa.

Leave a Reply