‘Yan sanda sun tsare Daraktan ma’aikatar ruwa da wasu mutum 2 kan zargin karkatar da injina a Kano

0
130

’Yan sanda sun tsare Daraktan Ma’aikatar Ruwa ta Kano kan zargin karkatar da injinan rarraba ruwan sha a jihar.

Alfijir labarai ta rawaito Abubakar Gambo ya shiga hannun ’yan sanda ne tare da wasu mutane biyu kan zargin su da yin takardun bogi na smaun izinin yi gwanjon wasu manyan injinan rarraba ruwan sha da kuma tankuna.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hussaini Muhammad Gumel, ya ce mutanen sun shiga hannun ne bayan Kwamishinan Ruwa na jihar, Ali Makoda, ya musanta ba da izinin sayar da injinna ruwan da kuma tankuna, yana mai cewa tsantar damfara ce suka shirya.

CP ya ƙara da cewa rundunarsa na ci gaba da bincike kan lamarin domin gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban ƙuliya.

KU KUMA KARANTA: Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya bada umarnin kamo sufeton da ya harbi mutane uku a Kurna

Sauran waɗanda aka kama su ne Mataimakin Sakataren Gudanarwa, Baba Yahaya da kuma Nuhu Mansir, wanda tsohon Manajna Shirin Noman Rani a  KAREFA ne a ƙaramar hukumar Tudun Wada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here