No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan sandan Najeriya sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, domin ƙwato motoci da ake zargin tsohon gwamnan ya tafi da su.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa a lokacin da aka kai samame gidan Matawalle a ranar Juma’a, an ce ‘yan sandan sun ƙwato Motoci guda huɗu na ‘Sport Utility Vehicles’ (SUVs).

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, amma bamu yi nasara ba, zuwa haɗa wannan rahoto layinsa a kashe.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta bai wa Matawalle wa’adin mayar da motocin alfarma na biliyoyin nairori

Idan za a iya tunawa, gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya zargi tsohon gwamna Matawalle da tserewa da motocin gwamnati tare da wawashe kadarori da suka haɗa da talabijin da kayan aikin dafa abinci a gidan gwamnatin jihar.

“Tsohon Gwamna Bello Matawalle ya tafi da motoci 17 daga ofishinsa da kuma waɗanda ke ofishin mataimakin gwamna yana mai cewa motocin kayansa ne.

Hasali ma kayan ofis ma ba a tsira ba. “Ta’addancin ya wuce fahimta, ban taɓa ganin rashin imani irin wannan ba.

Amma ina tabbatar wa ‘yan jihar cewa za mu yi iya ƙoƙarinmu don ganin mun gyara matsalar,” in ji gwamna Lawal.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...