Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne, su biyar, tare da cafke guda ɗaya tare da ƙwato dabbobi 143 a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar wa manema labarai hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.
Ya ce rundunar a wani samame da jami’an leƙen asiri suka gudanar, sun kai samame tare da tsarkake sansanonin ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin biyu da abin ya shafa.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna
Aliyu ya ƙara da cewa an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar mafarauta da ’yan banga.
“Kwamandan rundunar ‘yan sandan da ke kula da sashin yaƙi da garkuwa da mutane da kuma na ofishin bincike na musamman (SIB) ne ya jagoranta.
“Tawagar ta yi nasarar fatattakar wasu sansanonin ‘yan bindiga da dama a ƙauyukan Marake, Garin Yara da Garin Labo, duk a ƙaramar hukumar Batsari.
“Rundunar ta kuma tarwatsa wani sansanin wani Audu Lankai, wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga da ke addabar Jibiya da kewaye,” in ji shi.
A cewarsa, a yayin farmakin an kama wani Abubakar Idris, mai shekaru 18, wanda ake zargi da aikata manyan laifuka, yayin da aka kashe wasu biyar.
Ya kuma bayyana cewa an ƙwato shanu 38, tumaki 40 da awaki 65 a sansanonin ‘yan ta’addan.
Aliyu ya ce har yanzu ‘yan sanda na ci gaba da binciken inda lamarin ya faru domin ganin an kama wasu ‘yan sansanin ko kuma a ƙwato gawarwakinsu.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan yana ƙira ga mazauna jihar da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai a wani yunƙuri na daƙile ayyukan miyagun ayyuka a jihar.