‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu a Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa, rundunar ta ɗauki matakin daƙile wasu ‘yan bindiga guda biyu tare da daƙile wani hari da aka kai wa wasu al’umma a ƙaramar hukumar Tsafe.

Wata sanarwa a ranar Litinin a Gusau ta hannun Kakakin Rundunar, CSP Muhammad Shehu, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan, Kolo Yusuf ya yaba da jajircewar ‘yan sandan.

Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar ta himmatu sosai wajen daƙile sake bullar miyagun laifuka a faɗin jihar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Sanda sun kama ɗan gidan yarin Kuje da ya gudu

“An fatattaki ‘yan bindigar da suka yi yunƙurin kai wa al’umma hari, inda aka kashe biyu daga cikin waɗanda ake zargin ‘yan bindigar ne, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga.

“Kwamishanan ‘yan sandan ya kuma yaba da ƙoƙarin haɗin gwiwa da ‘yan sanda da sojoji ke yi a jihar, domin daƙile matsalar ‘yan fashi da makami da sauran miyagun laifuka,” in ji shi.

Shehu ya yi ƙira ga jama’a da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya a ƙoƙarin da suke na maido da dawwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da inganta tare da ɗorewar yaƙi da ‘yan bindiga a jihar.


Comments

2 responses to “‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu a Zamfara”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu a Zamfara […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga biyu a Zamfara […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *