‘Yan Sanda sun kama ɗan gidan yarin Kuje da ya gudu

1
274

Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa ta kama Salisu Buhari, ɗaya daga cikin fursunonin gidan gyaran hali na Kuje da ya tsere daga gidan yari a watan Yulin 2022.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakin rundunar ‘Yan Sandan jihar Nasarawa, Ramhan Nansel a ranar Lahadi a Lafiya. Mista Nansel, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce an kama Buhari ne tare da abokinsa Zubairu Ali bisa zargin satar babur a ƙaramar hukumar Nasarawa da ke jihar.

“A ranar 6 ga Afrilu, da misalin ƙarfe 10:00 na dare, jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin Nasarawa sun cafke wanda ya gudu bisa laifin satar babur. “Bincike na farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sune ke da alhakin mafi yawan satar babura a ƙaramar hukumar Nasarawa da kewaye.

KU KUMA KARANTA: Aregbesola ya gargaɗi ma’aikatan gidan yari kan cin hanci da rashawa

“Da aka yi masa tambayoyi, Salisu Buhari ya amsa cewa ya tsere daga gidan yarin Kuje lokacin da aka kai hari a shekarar da ta gabata.

Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa, “Wanda ya gudun, ya ce ya haɗa kai da muƙarrabansa bayan ya tsere daga wurin kuma ya shiga harkar aikata laifuka,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Maiyaki Muhammed-Baba ya bayar da umarnin miƙa ƙarar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, domin gudanar da cikakken bincike.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, a ranar 9 ga watan Yuli, 2022, rundunar ‘yan sandan jihar ta kama ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere, Hassan Hassan.

1 COMMENT

Leave a Reply