‘Yan sanda sun kama wata mata da ta yanka ‘yar aikinta da wuƙa a Legas

1
265

‘Yan sanda a jihar Legas sun kama wata mata ‘yar shekara 30 mai suna Eucharia Ndigwe da ta yi amfani da wuƙa wajen yi wa ‘yar aikinta ‘yar shekara 15 mummunar rauni, sakamakon rashin wanke jaka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya ranar Lahadi a Ikeja cewa an kama matar mai ɗauke da juna biyu a ranar Asabar.

Ya ce an kai Misis Eucharia zuwa sashin mana rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Rundunar ta kuma haɗa kai da hukumar yaƙi da cin zarafi ta jihar Legas domin ba ta kulawar lafiya.

Mista Hundeyin ya kuma shaida wa NAN cewa ‘yar aikin tana kwance a asibitin ‘yan sanda da ke Ikeja.

“A halin yanzu tana samun isasshiyar kulawar lafiya a asibitin ‘yan sanda da ke Ikeja.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama matar da ta gudu bayan ta daɓa wa yarinya ‘yar shekara 8 wuƙa

“Rundunar ‘yan sandan Legas ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da cin zarafin mata a faɗin jihar,” in ji Mista Hundeyin.

Ya ƙara da cewa kwamishinan harkokin mata na Anambara, Ify Obinabo, ta ziyarci yarinyar da ta tsiran ranar Lahadi a asibiti.

Kwamishinan ya samu rakiyar jami’ar da ke kula da sashin mata na ‘yan sanda, CSP Grace Agboola, wadda a halin yanzu take gudanar da shari’ar.

“Kwamishiniyar ta ce ta yi matuƙar farin ciki kuma ta yaba wa rundunar ‘yan sandan jihar Legas da gwamnatin jihar da kuma babban sufeton ‘yan sanda bisa ƙoƙarin da suka yi na ceto ‘yar aikin.

“Ta kuma ce gwamnatin jihar Anambara, jiharta ta haihuwa, a shirye take ta ba ‘yar aikin mafaka da kuma ba ta rayuwa mai ma’ana, ciki har da tura ta makaranta.

“Kwamishiniyar ta ce tana son Eucharia, wadda ake zargin ta yi wa ‘yar aikin rauni a gurfanar da ita,” in ji Mista Hundeyin.

1 COMMENT

Leave a Reply