‘Yan sanda sun kama wani mutum kan yaɗa hotunan tsiraicin na masoyiyarsa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta cafke wani ɗan kasuwa, Amarah Kennedy, wanda ake zargi da yaɗa hotunan tsiraicin masoyiyarsa a shafukan sada zumunta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama shi a shafin sa na Twitter a ranar Juma’a.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a.
A cewarsa, ana ci gaba da gudanar da bincike.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, wanda ake zargin yana cin zarafin ta da hotunanta na tsiraici.

KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yan sandan Legas ta kori jami’in da ya saci jaririya

Matar, wanda bazawara ce, wadda ta haɗu da Kennedy a Facebook, ya yi lalata da ita a wani otel inda aka ɗauki hotunanta na tsiraici ba tare da saninta ba.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya buƙaci Naira 140,000 daga gare ta a matsayin sharaɗin ɓoye hotunan amma ya karya alƙawarin bayan ya karɓi kuɗin.

Mista Kennedy, bayan ya wallafa hotuna 50 na tsiraici, ya ci gaba da neman ƙarin kuɗi yayin da ya yi barazanar ƙara sakawa idan ta ƙi yin hakan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *