‘Yan sanda sun kama wani matashi a Adamawa da laifin lalata da zakara

0
118

Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wani Lawali Mori mai shekaru 17 da haihuwa mazaunin Viniklang da ke ƙaramar hukumar Girei a jihar bisa zarginsa da lalata da zakara.

‘Yan sanda sun ce an kama shi ne saboda abin da ya yi ya saɓa wa tsarin halitta.

An kama Mori ne bayan wata Esther Dimas, mazaunin Viniklang, ta kama shi yana lalata da zakara, sannan ta kai rahoto ga ‘yan sanda dan gano lamarin da ya kai ga kama Mori.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Katsina ya umarci a binciki malamin da yayi lalata da ɗalibarsa a Ɗandume

A cewar sanarwar da rundunar ‘yan sandan Adamawa ta raba a shafinta na ‘X’, yayin da wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi lalata da zakara, kuma bai iya ba da dalilin yin hakan ba.

Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, yayin da yake nuna damuwarsa kan lamarin, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here