Jami’an tsaro a Najeriya sun bayyana yadda suka kama wasu ‘yan bindiga da ake zargin su da hannu a sace ɗaliban Jami’ar Jos da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.
‘Yan bindigan biyu na cikin mutum 91 da aka kama kan aikata mugayen laifuka daban-daban a yankin, a yayin da dakarun tsaro ke zafafa kai samame kan wasu ƙungiyoyin masu tayar da zaune tsaye.
An kama waɗanda ake zargi da sace mutanen ne bayan wani samame da aiki na musamman da aka ƙaddamar na tsawon wata guda, da suka yi sanadin da jami’an tsaro suka gano maɓoyarsu, kamar yadda mai magana da yawun wata rundunar soji ta musamman a Jihar Filato da ake ƙira Operation Safe Haven ya faɗa a wata sanarwa.
Sace-sacen mutane don karɓar kuɗaɗen fansa inda har ɗaliban jami’a ma ba su tsira ba, ya zama ruwan dare a Nijeriya.
KU KUMA KARANTA: Sojin ruwa ta kama kwale-kwale ɗauke da muggan ƙwayoyin miliyan 200
An saki waɗanda aka sace daga Jami’ar Jos ɗin bayan da iyayensu suka bai wa ɓarayin wasu kuɗaɗe da ba a faɗi yawansu ba, kamar yadda kafafan yaɗa labaran ƙasar suka ce.
Satar mutane don karɓar kuɗin fansa da ‘yan bindiga ke yi har yanzu wani babban ƙalubale ne ga jami’an tsaro a Nijeriya, inda a wasu lokutan har a kan kashe mutanen da aka sace ɗin.
‘Yan sandan Nijeriya na ba da shawarar cewa bayar da kuɗin fansa da ake yi ga masu satar mutanen kan rura wutar matsalar, inda suke gaya wa iyalan waɗanda aka sace cewa su daina biyan kuɗin fansar.
A hannu guda kuma, dakarun tsaro a Jihar Filaton sun ce an gano gawar wani shugaban wata al’ummar Fulani da ake ta nemansa.
An gano gawar shugaban al’ummar Fulanin na yankin Panyam, Arɗo Adamu Idris ne bayan da aka shafe kwanaki ana neman sa ba a gan shi ba.
Dakaru sun yi amfani da “sahihan bayanan sirri da mutanen yankin suka bayar,” a cewar wani mai magana da yawun sojoji Captain Oya James, a wata sanarwa da ya fitar.
“Tuni aka miƙa wa iyalan mamacin gawar tasa don a yi masa sutura,” ya faɗa. Har yanzu ba a gano waɗanda ke da hannu a kisan shugaban Fulanin ba, amma dama tsawon shekaru yankin yana fama da rikicin ƙabilanci da kuma matsalar satar mutane da gungun masu aikata laifuka ke yi.
“A yanzu za a ci gaba da bincike da fatan za a gano waɗanda suka aikata hakan tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya,” a cewar Kyaftin James.