Jami’an rundunar ‘yan sanda sun kama Fatima Auwal, shugabar matan da jagoranci masu gurasar da suka gudanar da zanga-zangar lumana , a Kano a makon daga gabata.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jakara ce ta kama shugabar a ranar Asabar.
Zanga-zangar da masu yin gurasar suka yi a Kano ranar Alhamis sun yi ne kan tsadar farashin fulawa.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Fatima Auwal ne biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da ‘yan sanda suka samu daga wasu mata biyu da wani mutum da suka ce ita ba ‘yar kungiyarsu ba ce, don haka ba ta da hurumin yin amfani da sunan su har ta jagoranci zanga-zanga .
Sai dai daga baya an sake ta a matsayin beli da yamma bayan wasu sun shiga maganar, ta kuma bukaci ta dawo ofishin ‘yan sanda a yau Lahadi.
Da take zantawa da SOLACEBASE kan lamarin, Fatima Auwal, ta ce ta yi mamakin tambayar da ‘yan sanda suka yi mata kan zanga-zangar lumana da ta yi da nufin faɗawa gwamnati mawuyacin hali da suka shiga sakamakon tashin farashin fulawa.
” ‘Yan sandan sun ce wasu mata da wani mutum ne suka yi ƙorafin cewa mun yi amfani da sunan ƙungiyarsu yayin zanga-zangar wanda hakan ba gaskiya ba ne”, a cewar Fatima Auwal.
KU KUMA KARANTA: Masu gurasa sun yi zanga-zanga kan tsadar fulawa a Kano
‘’Mutanen da suka shigar da ƙorafin su ne masu sayar da gurasa ne, alhali mu kuma mu ne masu hada gurasar. Don haka ya ba ni mamaki cewa sana’ar da mutane da yawa suka san mu akai za’a ce munyi sojan gona akan ta.’’
‘’Eh ‘yan sanda sun nemi da in dawo ofishina yau bayan an sake ni a matsayin beli jiya da daddare.
Da yake mayar da martani kan wannan al’amari, Shugaban ƙungiyar Jakara Junction Gurasa Bakers, Multi-Purpose Cooperative Society, Hadiyyatulahi Hamisu ya tabbatar da cewa su ne suka shigar da ƙorafin a wajen ‘yan sanda kan amfani da sunan kungiyarsu da masu zanga-zangar suka yi.
Ko da yake Hamisu ya ce shugabar zanga-zangar, Fatima Auwal ita ma mai yin gurasa ce kuma ita ce shugabar ƙaramar ƙungiyar masu gurasa.
”Shi ya sa muka kai ƙarar ‘yan sanda.” ”Abin da muke nema a gare ta shi ne ta koma kafafen yaɗa labarai ta janye maganarta.”
Hadiyyatulahi wanda shi ma ya tabbatar da hauhawar farashin na fulawa, ya ce kalubalen tattalin arziki ne na yau da kullum da ake fuskanta a ko ina.