‘Yan sanda sun kama shugaban ƙabilar Igbo da yayi barazanar gayyato ‘yan ta’addan IPOB zuwa Legas

Fredrick Nwajagu, shugaban ‘yan ƙabilar Igbo wato Eze Ndigbo na yankin Ajao Estate a jihar Legas ya shiga hannun jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS a wani samame da suka kai masa da safiyar yau Asabar.

An kama Nwajagu ne bayan bayyanar wani faifan bidiyo da ya nuna shi yana tofa albarkacin bakinsa tare da shirin gayyatar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (‘yan ta’addan IPOB) zuwa Legas domin su kare kadarori da kasuwanci na ƙabilar Igbo.

Eze Igbo na Ajao ya faɗa a cikin faifan bidiyon a ranar Juma’a, 31 ga Maris, inda ya yi barazanar cewa, “IPOB, za mu gayyace su”.

KU KUMA KARANTA: Budurwa ‘Yar IPOB da ta ƙware a kisan mutane ta shiga hannu

“A yanzu ba su da aiki, don haka zamu gayyato su (IPOB) su zo Legas domin kare dukkan shaguna da ɗaukacin dukiyoyinmu, kuma dole ne mu biya su, dole ne mu haɗa kai don yin haka, dole ne mu yi hakan.

“Dole ne mu sami namu tsaro domin su daina kai mana hari da tsakar dare, da safe, da kuma rana, lokacin da suka gano cewa muna da namu tsaron, kafin su zo, za su san cewa muna da namu shirin, kuma mun ajje maza a can.

“Ba zan faɗi kalma ɗaya da za a ɓoye ba, a ina ɓoye maganata ba; bari kalmomi na su tafi a hoto ko bidiyo mai zagaya yanar gizo cikin sauri.

“Dole ne Igbo su sami ‘yancinsu kuma su tsaya a jihar Legas.” In ji basaraken.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗab bayan wani ɓangare na ‘yan awaren kuma shugaban IPOB na kasar Finland, Simon Ekpa, ya yi barazanar sanya dokar zaman guda a jihar Legas bisa zargin ƙona shagunan ‘yan kabilar Igbo a wani yanki na jihar.

A baya-bayan nan ne kungiyar IPOB ta kasance ta 10 a jerin ƙungiyoyin ta’addanci a duniya.


Comments

2 responses to “‘Yan sanda sun kama shugaban ƙabilar Igbo da yayi barazanar gayyato ‘yan ta’addan IPOB zuwa Legas”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama shugaban ƙabilar Igbo da yayi barazanar gayyato ‘yan ta’addan IPOB zuwa L… […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama shugaban ƙabilar Igbo da yayi barazanar gayyato ‘yan ta’addan IPOB zuwa L… […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *