No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wani magidanci mai shekaru 56 da laifin lakaɗawa tsohuwar matarsa ​​mai shekaru 38 dukan tsiya, ta mutu har Lahira a lokacin da ya samu labarin za ta sake yin aure washegari.

Wanda ake zargi da kisan kai mai suna Aminu Abubakar, mazaunin Lelewaji, Shagari Estate a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu, an bayyana cewa ya fuskanci Nana Faɗimatu da misalin ƙarfe 10 na daren Juma’a da bayanin cewa za ta yi aure.

Labarun Fombina sun gano cewa ma’auratan sun yi aure shekara tara suna da yaro ɗaya kafin su rabu.

Ya fusata ya fara dukanta da wani abu mai kauri. Ta faɗi a sume ta mutu daga baya.

KU KUMA KARANTA: Matashi ya kashe mahaifiyarsa a Kano

Lokacin da angonta, Mahmud Rufa’i, mazaunin Shagari Annex, a ƙaramar hukumar, ya samu labarin faruwar lamarin, ya kai ƙararsa ga ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Shagari.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Sulaiman Nguroje ya fitar, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa Afolabi Babatola ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...