Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum uku da ke cikin wani gungun masu ɗauke da bindigogi da ya kai hare-hare a jihar Filato a jajibirin Kirsimeti waɗanda suka yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 200.
A wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Talata da maraice, ya ce mutanen na cikin mutum 67 da suka kama bisa zargin aikata laifuka daban-daban a faɗin ƙasar.
“Mutanen da ake zargin su ne Ahmed Sulaimon da Balikisu Aliyu da Aboki Samuel. Bayan an kama su, an gano makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da ƙirar AK-49 guda ɗaya da harsasai 1000 da kwanson harsasai biyar,” in ji Adejobi.
Ya ƙara da cewa “a halin da ake ciki mutanen suna tsare a hannun ‘yan sanda kuma suna taimakawa wurin bincike.
KU KUMA KARANTA: An kafa wata rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato
Wasu ‘yan bindiga ne suka ƙaddamar da jerin hare-hare a ƙauyuka kusan ashirin a jihar ta Filato a jajibirin Kirsimeti.
Tun da fari, hukumomi sun ce mutum 163 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos.
Sai dai yayin da mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara a jihar ta Filato, shugaban ƙaramar hukumar Bokkos Monday Kassah ya ce mutum 148 aka kashe a yankinsa.
Kazalika an kashe mutum aƙalla 50 a ƙauyuka daban-daban na ƙaramar hukumar Barkin Ladi, a cewar Dickson Chollom, wani ɗan majalisar dokokin jihar daga yankin.
“Muna rokonku da ku guji raba kawuna da kiyayya ga junanku, a yayin da muke kokarin ganin an yi adalci domin samar da zaman lafiya,” in ji Kashim Shettima a yayin da ya gana da jami’an gwamnati da sarakuna da kuma mazauna yankunan.
Olumuyiwa Adejobi ya ƙara da cewa a yunƙurin rundunar ‘yan sanda na kakkaɓe aikata laifuka a faɗin ƙasar nan, sashen leƙen asiri da dabaru ya yi nasarar kama mutum “67 da ake zargi da aikata laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane da sayar da makamai, da fashi da makami.”
“Kazalika ‘yan sanda sun ƙwace harsasai 5,454 da kwanson harsasai 300 da ƙananan bindigogi 68 da katin cirar kuɗi na ATM 33 da sauransu,” in ji kakakin ‘yan sanda.