‘Yan sanda sun kama mutane 2 da satar janareto da batirin solar masallaci

0
124

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar janareta da batir mai amfani da hasken rana a wani masallaci da ke Kaduna.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna ranar Asabar.

Hassan ya ce a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, bisa samun sahihan bayanai, jami’an ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin tare da kai shi ofishin unguwar Sabon Garin da ke ƙaramar hukumar Hunkuyi a jihar.

Hassan ya ce, “An kama wanda ake zargin ne da laifin sata a cikin masallacin.”

KU KUMA KARANTA: Baƙuwa ta sace jariri awa 3 da haihuwarsa a asibiti

A cewarsa, a yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa laifin satar janareta da batir mai amfani da hasken rana a ƙauyen Hunkuyi da ƙauyen Nahuce a cikin masallacin su.

“Wanda ake zargin ya ci gaba da cewa ya sayar da kayan da ya sata ga wanda ake zargi na biyu .

“An gano wasu abubuwan da dama, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike,” in ji Hassan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here