Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wata mata mai suna Fatima Salisu ‘yar shekaru 35 da haihuwa bisa laifin daɓa wa wata yarinya ‘yar shekara 8 da haihuwa wuƙa a ciki.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya tabbatar da kamun a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a a Kano.
“A ranar 14 ga watan Mayu da misalin ƙarfe 6:40 na yamma ne aka samu ƙiran gaggawa daga wani mutumin kirki, cewa ya ji kukan wata yarinya daga wani gini da ba a kammala ba da ke Kureken Sani a ƙaramar hukumar Kumbotso.
“Mutumin ya garzaya wurin da lamarin ya faru inda ya tarar da yarinyar a cikin jini da aka caka mata wuƙa mai kaifi a ciki, wuƙar ta maƙale a cikinta da kuma raunuka a wasu sassan jikinta.
KU KUMA KARANTA: Za a rataye wani ɗan aiki da ya kashe tsohuwa, da ‘yarta
“Da samun labarin, an ceto Sharifa ‘yar shekara 8 a Gadon Ƙaya Quarters Kano, aka garzaya da ita asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano inda aka kwantar da ita.
Nan take kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini-Gumel, ya ba da umarnin a jami’an ‘yan sanda tare da yin amfani da duk ƙarfi da suke da su don tabbatar da cewa an kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika da gurfanar da su, da zarar an kama su.
“Ci gaba da bin diddigin aiki tare da jami’an leƙen asiri sun kai ga cafke wanda ake zargin a wata maɓoya a ƙauyen Dungulmi da ke gundumar Isari a jihar Dutse a ranar 18 ga watan Mayu.”
Haruna-Kiyawa ya ce yarinyar da take jinya a asibiti ta bayyana matar da ta daɓa mata wuƙa a matsayin wata Fatima da ke zaune a unguwarsu.
Ya ce yarinyar ta sanar da ‘yan sanda cewa wanda ake zargin ta ɗauke ta ne daga Gadon Ƙaya Quarters zuwa ginin da ba a kammala ba a Kureƙen Sani.
Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa, “Wacca ake zargin ta daɓa mata wuƙa a wuyanta, cikinta, ta bar wuƙar maƙale a cikinta, ta barta sannan ta gudu daga wurin.”
Ya ce yayin gudanar da bincike na farko, an kama mijin wanda ake zargin, Yusuf Aminu na Gadon Ƙaya Quarters. “Aminu ya yi iƙirarin cewa matarsa (wacca ake zargin) tana da taɓin hankali kuma bai san inda take ba.”
Haruna-Kiyawa, ya ce wacce ake zargin ta amsa cewa ta daɓa wa yarinyar wuƙa ne don ramuwar gayya, saboda mahaifin wanda aka ji wa ciwon, na ba mijinta shawarar ya ƙara aure.
“Ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da ita a kotu.
“Kwamishinan ‘yan sandan ya yaba wa waɗanda suka taimaka da bayanan da suka kai ga kama wacce ake zargin,”
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama matar da ta gudu bayan ta daɓa wa yarinya ‘yar shekara 8 wuƙa […]