‘Yan sanda sun kama kwarto da rana tsaka a Ogun

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani Godstime Ekanem da ake zargi da shiga gidan auren wata mata mai suna Misis Jelila Oyinbo tare da yunƙurin yi mata fyaɗe.

Kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 28 ga Satumba, 2023, ya ce lamarin ya faru ne a Mowe-Ofada, ƙaramar hukumar Obafemi Owode ta jihar.

A cewar PPRO, matar ta ce Ekanem yana yi mata zancen banza na neman lalata da ita duk da gargaɗin da ta sha yi masa na ya rabu da ita saboda ita matar aure ce.

Sai dai wanda ake zargin ya dage, kuma a ranar Talata, 26 ga watan Satumba, ya shiga gidan matar ne a lokacin da mijinta ya fita.

KU KUMA KARANTA: Wani Dattijo ya yi wa yarinya kurma fyaɗe ta mutu

“Yau 28 ga watan Satumba, 2023 wata Misis Jelila Oyinbo “F” ta kamfanin MTN Estate a Mowe Ofada Jihar Ogun ta ruwaito cewa Godstime Ekanem ya yi ta takura rayuwarta na neman ya yi lalata da ita duk da ta yi masa gargaɗi cewa ita matar aure ce, amma Ekanem ya ƙi bari, ya tsaya tsayin daka kuma ya ci gaba da takura mata,” in ji sanarwar.

“A ranar 26 ga watan Satumba, 2023 da misalin ƙarfe 08:00 na safe, ya fahimci mijin nata ya bar gida, sai Ekanem ya shiga gidan aurenta ya kai mata hari da nufin ya yi lalata da ita.

“Ta yi ta kokawa da shi inda ta sanar da surikinta Michael Oyewole wanda ya garzaya gidan don ceto Jelila, yayin da Ekanem ya ɓoye kansa.

Micheal ya yi fafata wa da Ekanem a cikin ɗakin inda ya kwaɗa mashi guduma a kai,  Michael ya rama ta hanyar sare Ekanem da adda a kai’.

“Ekanem ya gudu ya bar wayarsa da silifas a ɗakin matar.

“‘Yan sanda sun kama Ekanem yayin da aka kai Micheal Oyewole asibiti domin kula da lafiyarsa.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *