‘Yan sanda sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a Kwara

1
343

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da ceto wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Isin ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ajayi Okasanmi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Ilorin.

Sanarwar ta ce, tawagar ‘yan sanda da mafarauta da ’yan banga ne suka ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ebunoluwarotimi Adelesi.

“Duk da haka, bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda na jihar, rundunar ‘yan sandan da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane da ke a yankin Isanlu-Isin, tare da taimakon mafarauta da ’yan banga, suka fantsama tare da bai wa waɗanda suka sace garkuwan suka fatattake su.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun ceto ɗalibai shida daga cikin bakwai da aka sace a Jami’ar Jos

“A cikin haka ne masu garkuwa da mutanen suka yi watsi da motar Sienna da ke jigilar waɗanda abin ya rutsa da su a lokacin da lamarin ya faru kuma rundunar ta ceto ɗaya daga cikinsu mai suna Oke Olatunji.

“Kwamishinan ‘yan sanda da kansa ya jagoranci wata tawaga ta musamman kan aikin bincike da ceto cikin dajin da ke cikin garin Isin, kuma ana cikin haka, an ceto wani wanda abin ya shafa mai suna Femi Ajayi, da harbin bindiga.

“An kai shi cibiyar lafiya da ke Isanlu-Isin inda a yanzu haka yake samun kulawar likitoci.

“Yan sanda sun ceto wasu mutane biyu a daren Asabar 15 ga watan Yuli,” sanarwar ta ƙara da cewa a wani ɓangare.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya tuna cewa a ranar 13 ga watan Yuli, an sace wasu mutane huɗu Dipe Ajayi, Kunle Abolarin, Femi Abolarin da Femi Ajayi da misalin ƙarfe 5 na yamma a Isanlu-Isin.

Waɗanda abin ya shafa sun fito ne daga Oke-Arin, Isanlu-Isin a òaramar hukumar lsin ta jihar.

1 COMMENT

Leave a Reply