‘Yan sanda sun cafke wani ɗan fashi da ake nema ruwa a jallo

0
299

A ranar 17 ga watan Oktoba 2023, rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta yi nasarar cafke wani ɗan fashi da aka daɗe ana nema ɗan kimanin shekara 30 mai suna Shu’aibu Abubakar. Shua’aibu dai ya kasance cikin jerin waɗanda rundunar take nema ruwa a jallo tun da daɗewa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, shi ne ya bayyana hakan a shafin su na X a ranar Laraba.

Sanarwar ta fito kamar haka, “An kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Shuaibu Abubakar, kamen dai ya biyo bayan wani samame da jami’an ‘yan sandan jihar tare da haɗin gwiwar mafarauta suka yi a ranar Talata.

“Wanda aka kaman ya fito ne daga garin Tambo na ƙaramar hukumar Girei kuma ya kasance cikin jerin waɗanda rundunar ke nema ruwa a jallo.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a jihar Yobe sun kama wasu da ake zargi da fashi da makami a jihar

“A tare da ɗan fashin, an ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya ɗauke da harsashi goma sha shida.”

kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Afolabi Babatola, a lokacin da yake bayyana tsantsan farin cikinsa, ya bayyana cewa, masu aikata laifuka ba su da mafaka a jihar Adamawa, saboda rundunar ta shirya zaƙulo ta’asar satar mutane da aka tafka a jihar a cikin watannin baya.

Leave a Reply