‘Yan sanda sun cafke shugaban ƙungiyar ƙwadago na Najeriya

‘Yan sanda sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago na Nijeriya (NLC) Joe Ajaero, a birnin Owerri na Jihar Imo.

Kakakin ƙungiyar Benson Uper ne ya bayyana haka a saƙon da ya aike wa manema labarai ta manhajar WhatsApp. Kawo yanzu ba a san inda aka nufa da shi ba.

NLC tana jagaranci zanga-zanga a faɗin jihar ta Imo game da abin da ta ƙira rashin kyautata wa ma’aikata da hana su albashi da sauransu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *