‘Yan sanda sun cafke mutumin da ya yi yunƙurin cinnawa masallaci wuta

1
349

‘Yan sanda sun cafke wani mutum da ya yi yunƙurin cinnawa wani masallaci wuta a birnin Dresden na ƙasar Jamus da yammacin jiya Talata.

Mutumin ya zubar da fetur a gaban wani masallaci kuma ya yi ƙoƙarin cinnawa ginin wuta, in ji kakakin ‘yan sandan.

Shaidu sun ƙira lambar hukumar bayar da agajin gaggawa bayan da suka ga mutumin yana zuba man fetur a wajen masallacin, wanda a lokacin ya cika.

KU KUMA KARANTA: Yadda kaka ta cinna wa ɗanta, matar shi da jikokin ta wuta a Ondo

An kama mutumin mai shekaru 34, kuma yana ƙarƙashin binciken ‘yan sanda kan yunƙurin tada ƙayar baya.

Duk da cewa da farko ba a san dalilinsa ba, an ce wanda ake zargin ya ƙona kwafin Alƙur’ani mai girma a wani masallaci a watan Afrilu.

1 COMMENT

Leave a Reply