No menu items!

Sample Page Title

Date:

’Yan sanda sun kama wasu matasa bakwai kan laifin yin sojan gona da kuma layu 582, a garin Kaltungo a jihar Gombe

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce dubun waɗanda ake zargin ta cika ne inda aka kama su da makamai da tabar wiwi da tulin ƙwayoyi daban-daban.

Ya ce an kama matasan, masu shekaru 17 zuwa 21 ne a wani samame da ’yan sanda suka kai wata maboya a kasuwar garin Kalarin da Baganje a ƙaramar hukumar Kaltungo, a ranar 3 ga watan Disamba 2023.

Ya ce abubuwan da aka samu a wajen su a matsayin kayan shaida sun haɗa kakin soja guda ɗaya da hula hana-sallah, gidan harsashin bindiga kirar AK 47, da takubba da wuƙaƙe da kuma gatari.

Sauran sun haɗa wuƙaƙe da ƙwayar exzol, ƙulli 19 na tabar wiwi, kati 40 na kwayar Tramadol, layu guda 582, da kuma wata riga da aka ɗinka ta da layu.

Daga nan sai ya ce akwai sauran matasan da zargin, waɗanda rundunar ke ci gaba da kokarin kamo su domin fuskantar shari’a.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...