’Yan sanda sun ƙira riƙaƙƙun ’yan daba 52 sulhu a Kano

0
160

’Yan sanda sun gayyaci wasu jagororin ’yan daba 52 domin yin sulhu da su a ƙaramar hukumar Ƙiru ta jihar Kano.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, Hussaini Muhammadu Gumel ne ya sanar da hakan a wani zama da ya yi da masu ruwa da tsaki a yankin Kwanar Dangora da ke ƙaramar hukumar Ƙiru.

Kwamishinan ya yi ƙira ga mahalarta zaman da su ba da haɗin kai wajen samar da wanzajjen tsaron rayuka da dukiyoyi a ƙaramar hukumar da ma Jihar Kano baki ɗaya.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ruwaito shi yana cewa, mahalarta taron sun taimaka wajen gano manyan ’yan daba guda 52 da ake nema a yi sulhu da su, saboda suna da hannu wajen tayar da zaune tsaye a ƙaramar hukumar.

KU KUMA KARANTA: Muna ƙoƙarin kakkaɓe matsalar tsaro amma har yanzu ba mu yi nasara ba — Tinubu

CP Hussaini Gumel ya yaba wa sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da shugaban ƙaramar hukumar Ƙiru bisa haɗin kan da suke ba wa rundunar wajen samar da kwanciyar hankali a Kwanar Dangora, Karamar Hukumar Kiru da ma Jihar Kano.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana cewa, rundunarsa a shirye take wajen yaƙi da kuma murƙushe da duk wani nau’i na barazanar tsaro a faɗin Jihar Kano.

Leave a Reply