’Yan sanda mata sun tallafa wa marayu 300 a Gombe

0
132

Wasu ’yan sanda mata a Jihar Gombe sun yi karo-karo kuɗaɗe suka sayi kayan abinci suka kai gidan marayu na Musulmi da na Kirista a unguwar Tumfure da ke fadar jihar.

’Yan sandan a karkashin jagorancin ASP Esther Musa, sun kai wa gidaje marayun buhunan masara da kwalayen sabulun wanka da omo da takalma da tsabar kuɗi.

Da take jawabi a gidan marayu na Kirista mai suna Christian Covenant & Orphans Foundation ASP Esther Musa, ta ce ƙungiyarsu mai suna Strong Binding ce ta ga ya dace su tara dan wani abu a tsakaninsu su tuna da marayu.

KU KUMA KARANTA: Wata bazawara a Kano, tana tura ruwa a baro, tana sayarwa domin ta ciyar da ‘ya’yanta marayu

Ta ce sun taimaka ne da ɗan abin da ya sauwaka domin ya fi ace ba su yi ba amma da son samu ne da abin da suka bayar ɗin yafi haka.

Da ya ke marabta su Daraktan gidauniyar ta Christian Covenant & Orphans Foundation Mista EL-Polycarp Y Degri, ya ce sun ji dadi bisa wannan dauki da ’yan sanda mata suka kawo musu domin da kowa zai dinga tunawa da yara marayu a irin waɗannan gidajen da za a samu saukin kula da su.

El-Polycarp, ya ce hatta tallafin abinci da gwamnati take bayarwa ba a taɓa ba su ba, irin waɗannan mata ’yan sanda da ƙungiyoyi ne suke kokari a kan su.

Ya ce gidan marayu na tumfure reshe ne nasu domin babban gidan yana garin Degri a ƙaramar hukumar Balanga inda suke da marayu 260 kuma duk tallafin da aka ba su suna rabawa gidajen ne kowa su samu.

A gidan marayu na Musulmai, sun ba da irin wannan tallafi inda shugaban gidan  Dokta Babayo Kolo, ya nuna jin daɗinsa matuƙa, musamman ganin cewa gwamnati ba ta taɓa ba su wani kuɗi ko kayan abinci na don kula da marayu ba,  amma ɗaiɗaikun jama’a da ƙungiyoyi sune masu kai musu tallafi.

Dokta Babayo Kolo, ya yi ƙira ga gwamanti da masu hannu da shuni da su yi koyi da ’yan sanlnda mata da suka kai musu wannan tallafi, ko da yake hakan ba abun mamaki bane domin mata sun fi tausayi wajen kula da yara.

Ya ce a halin yanzu suna da marayu 60 ne, sauran sun girma an aurar da su, mazan kuma sun balaga an yaye su.

ASP Esther Musa, ta ce da suka zo su ka bada kayan zuciyar su ta kaɗu matuƙa inda tace a shekara mai zuwa za su duba yiwuwar ƙara yawan abin da za su bayar.

Leave a Reply