No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai shekara 19 da zargin yi wa ‘yar uwarsa ciki a ƙaramar hukumar Tofa da kuma zargin haɗa baki wajen kashe ta.

Wata sanarwa daga runundar ta ce ta kama Ukasha Muhammed ne bayan ta samu rahoton cewa ya yi wa Amina Bala mai shekara 19 ciki, sannan ya kai ta wajen wani mai suna Chidera Ugwu don ya yi mata allurar zubar da cikin.

Sanarwar ta ce Mista Ugwu, wanda likitan bogi ne, ya yi mata allura tare da ba ta wasu ƙwayoyin magani don zubar da cikin, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Nijar

“An kama waɗanda ake zargin kuma sun amsa laifukan da ake zargin su da aikatawa,” in ji runudnar.

Ta ƙara da cewa da ma Ugwu ya saba yi wa mata masu ciki “allurar da ke kaiwa ga rasa rayukansu”.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...