‘Yan sanda a jihar Yobe sun hana sanya wa mota baƙin gilashi da rufe lambar mota

2
342

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ta haramta amfani da gilashin baƙi a motocin hawa da rufe lambobin mota da kuma lodin wuce ƙa’ida, musamman Keke NAPEP.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkareem ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Garba Ahmed, ya lura cewa masu Keke NAPEP a jihar sun ba da gudumawa sosai wajen aikata laifuka da kuma laifukan da suka shafi haɗurra.

Ya ce rahotannin sirri sun nuna cewa mutanen da ke da wasu munanan halaye suna fakewa da baƙin gilashin don aikata laifuka.

KU KUMA KARANTA: Hukumar kiyaye haɗurra ta FRSC, ta koka da yawaitar tudun taƙaita gudu akan hanyar Gombe zuwa Yola

Ya kuma ce masu ababen hawan da suka saba rufe lambobinsu ko cire su yana da wuya a gano ko wanene su a yayin da suka yi hatsari, ko keta haddi ko bayanan da jami’an tsaro ke buƙata.

Don haka ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da bin ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa da kuma ɗaukar matakan hukunta duk wanda aka samu da saɓa wannan doka.

2 COMMENTS

Leave a Reply