‘Yan sanda a Indiya, sun kama mutumin da ke jagorantar rajin kare haƙƙin shanu

0
332

Rundunar ‘yan sanda a jihar Haryana ta Indiya ta kama wani shahararren tsagera na addinin Hindu wanda ake zargi da tayar da husumar da ta haifar da kashe mutum shida.

Monu Manesar, wanda ke jagorantar masu tsattsauran ra’ayin Hindu, na cikin waɗanda suka assasa shirin kare shanu, waɗanda ke da martaba a addinin Hindu.

Ana zargin shi da haddasa rikici a lardin Nuh.

Haka nan ana zargin shi da jagorantar wani mummunan duka da aka lakaɗa wa wasu matasa musulmai a yankin Rajasthan.

Bayanai sun ce ya wallafa wasu bayanai na tayar da husuma a shafukan sada zumunta gabanin tattakin na mabiya addinin Hindu da aka yi a Haryana, wanda ya janyo tashin hankali.

Leave a Reply