‘Yan sanda a Indiya sun kama iyayen da suka yi wa yaransu auren wuri

0
204

Hukumomin Indiya sun kama sama da mutane dubu ɗaya a arewa maso gabashin ƙasar a ranar Talata a wani ɓangare na yaƙi da aurar da ƙananan yara a yankin a bana.

Tuni dai jihar Assam ta kame mutane 4,000 a wani yunƙuri da ta yi a watan Fabrairu, ciki har da iyayen yaran da suka yi aure da kuma ma’aikatan gwamnati waɗanda suka yi rajistar auren ƙananan yara.

Alƙaluman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa akwai ƙananan yara sama da miliyan 220 da suka yi aure a Indiya.

Duk da cewa al’amuran auren ƙanana yara sun ragu matuƙa a wannan ƙarnin, har yanzu al’adar tana yaɗuwa.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta raba auren wata 10 ta hanyar “Khul’i”

A cewar Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), kalmar auren yara tana nufin duk wani aure ko kuma wani tsarin zama tsakanin yaro da bai kai shekara 18 da wani babba ko yaro.

Babban Ministan Jihar Himanta Biswa Sarma ya sanar da cewa, ‘yan sanda sun ƙaddamar da wani samame na musamman wanda aka fara tun da sanyin safiya.

Ya wallafa a dandalin sada zumunta na X (wanda aka fi sani da Twitter): cewa “Yawancin adadin waɗanda ake tsare da su zai iya ƙaruwa,” wanda a halin yanzu adadin ya kai 1,039.

Leave a Reply