Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Gombe ta cafke wani matashin yaro ɗan shekara 18, Mustapha Adamu Isah, wanda aka fi sani da Abbati, bisa zargin kashe wata mata.
Jaridar The Nation ta ce ‘yan sanda sun kama Abbati, wanda ake zargi da halaka Hajiya Aishatu Abdullahi wacce ake ƙira da Damori a Unguwar Jekadafari Quarters da ke cikin Gombe.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mahid Mua’zu, shi ne ya bayyana haka yayin da yake nuna wanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda ranar Jumu’a.
Ya ce ranar Jumu’a 20 ga watan Oktoba, ‘yan sandan Caji Ofis ɗin Pantami suka samu ƙorafi daga ɗan matar cewa wani makashi da bai gane ko waye ba ya yi wa mahaifiyarsa yankan rago.
KU KUMA KARANTA: An kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata, ta hanyar yi mata yankan rago a Gwambe
Ya ce “Nan take jami’an Caji Ofis a Pantami suka kai ɗauki wurin, suka tarad da matar Aishatu Abdullahi, kwance cikin jini, suka ɗauke ta zuwa Asibitin koyarwa na Gombe inda aka tabbatar ta rasu.”
Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa an kama Abbati ranar 22 ga watan Oktoba, 2023 bisa zargin hannu a kisan matar bayan samun sahihan bayanan sirri daga tawagar bincike.
A cewarsa, a yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga ɗakin Aishatu Abdullahi ne domin neman sufanarsa da ta ƙwace.
Wanda ake zargin ya kuma ambaci abokinsa, Idris Abubakar Danjauro, mai shekaru 17, wanda ya ce ya zo ɗakin ya kama shi ya aikata wannan ɗanyen aikin.
Sai dai Idris, wanda aka kama daga baya, ya musanta cewa bai san wanda ya kashe matar ba a lokacin da bincike ya biyo ta kansa, Tribune ta rahoto.
Wanda ake zargin ya bayyana cewa Aishatu ta dawo daga maƙwabta, ta same shi a ɗakinta, ta tuhume shi tare da umartan ya fice mata daga ɗaki amma ya ƙi fita.”
“Wanda hakan ya sa ya afka mata, ya shaƙe ta, ya kashe ta da wuƙa, ya tsere ta bayan gida zuwa inda ba a sani ba.”