No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun cafke wani da ake zargin ɓarawon mota ne mai suna Ibrahim Mohammed mai shekaru 25 da laifin satar mota a wani Masallaci a ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023, ya ce jami’an da ke aiki a hedikwatar ‘yan sandan Tilden Fulani sun kama wanda ake zargin da motar da ya sace a kan babbar hanyar da ta haɗa jihohin Bauchi da Filato.

PPRO ya bayyana cewa wanda ake zargin wanda ya fito daga Unguwan Gyadi-Gyadi, jihar Kano, amma kuma yana zaune a Gwarinpa, FCT Abuja, ya amsa laifinsa kuma za a miƙa shi jihar Kaduna domin ci gaba da bincike.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...