‘Yan sanda a Abuja sun kama gawurtattun masu garkuwa da mutane

0
123

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kama wasu masu aikata laifuka a Abuja, ciki har da gawurtattun masu garkuwa da mutane.

Rundunar ta bayyana haka ne a saƙon da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar asabar da maraice.

Kakakin rundunar ta ‘yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya gabatar wa manema labarai mutum 16 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ya ce sun kama makamai da dama ciki har da mashingan.

“A cikin waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane da aka gabatar da su a yau akwai mutum uku da ke zaune a yankin Bwari – Idris Ishaku da Bala Umar da Dahiru Salisu, kowanensu dan shekara 27. Su ne suka yi jerin fashi da makami da satar jama’a a Ƙaramar Hukumar Bwari da sauran sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja,” in ji Adejobi.

KU KUMA KARANTA: An cafke ƙasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi yankin Abuja

Ya ƙara da cewar dakarun nasu sun kuma kama mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a babban birnin na Najeriya.

Kazalika rundunar ‘yan sandan ta Najeriya ta ce dakarunta na sirri sun daƙile wani yunƙuri na yin garkuwa da mutane lamarin ne me ya kai ga kama gawurtattun masu satar mutanen a Bwari da makamansu.

Ta ce ma’aikatanta sun kama wani mutum mai suna Everest Magaji, wanda yake sayar da makamai da yin garkuwa da mutane yayin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa, tana mai cewa wasu abokansa da ke da hannu a lamarin sun tsere. Sai dai ta ce an ƙwace makamai daga wurinsu.

Leave a Reply