Connect with us

Zaɓe

‘Yan sa kai sun maye gurbin ma’aikatan INEC da suka gaza zuwa aiki, a Anambra

Published

on

Wasu masu kaɗa kuri’a a Ozubulu da ke ƙaramar hukumar Ekwusigo a Anambra, sun ba da kansu a matsayin jami’an wucin gadi na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, bayan da waɗanda aka aiko suka kasa fitowa aikin zaɓen.

Masu aikin sa kai sun maye gurbin ma’aikatan wucin gadin ne domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe a rumfunan zaɓe 006, 007, da 008 a makarantar Uruokwe Central School da ke Ozubulu, ƙaramar hukumar Ekwusigo a ranar Asabar.

Rahotanni sun nuna cewa tun da farko wasu mambobin ƙungiyar da suka samu horo tare da tura su aikin zaɓe a rumfunan zaɓe ba su bayyana ba a ranar Asabar.

Sai dai shuwagabannin da ba ‘yan INEC ba ne suka bayar da rahoton yin aiki inda wasu masu kaɗa kuri’a suka ba da kansu don yin aiki a matsayin jami’an wucin gadi.

KU KUMA KARANTA: Kuɗi shine mabuɗin shirye-shiryen gudanar da aiki a ranar zaɓe – Jega

Hakan, ya haifar da ƙalubale yayin da masu aikin sa kai ba su da horo kuma suna da matsala wajen tafiyar da tsarin tantance masu kaɗa kuri’a (BVAS) da kuma bin tsarin da aka gindaya na atisayen.

Haka lamarin ya kasance a rumfunan zabe 018 da 019, a dakin taro na Umuanyiegbu, Ward 004, Ozubulu, Ekwusigo LGA. Shugabannin sun ƙi yin magana da ‘yan jarida da kuma ƙoƙarin ganin kwamishiniyar zaɓe ta INEC, Dr. Elizabeth Agwu, don ta bada bayani yaci tura.

Har ila yau a Enugu, an ga wasu masu aikin sa kai musamman matasa suna taimakawa wasu ma’aikatan wucin gadi wajen kafa rumfunan zaɓe da kuma tabbatar da tsaro a wasu yankunan jihar.

A Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Enugu, ɗaya daga cikin ‘yan agajin da aka fi sani da Nonso, ya bayyana cewa ya yanke shawarar taimakawa ne domin ganin an gudanar da zaben cikin sauki. “Na yanke shawarar taimaka don shawo kan ɗimbin jama’a.

Tun bayan gudanar da babban zaɓe a kasar nan ban taba ganin irin wannan fitowar jama’a ba. “Don haka, ni da abokaina mun sadaukar da kai don taimakawa tunda akwai jami’an tsaro kaɗan a rumfar zaɓe,” inji shi.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Ba zan sauka ba, shugaban INEC ga jam’iyyun adawa | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Zaɓe

Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Yobe — Jam’iyyun Adawa

Published

on

Mun shirya tsaf domin shiga wannan zaɓe amma kuma muna sara ne muna duba bakin gatarinmu.

A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a ranar Asabar ta ƙarshen wannan wata na Mayu a Jihar Yobe, wasu shugabannin jam’iyyun adawa da ke jihar da suka haɗa da Jam’iyyar NNPP da PDP da AD da PDM sun bayyana shirinsu na shiga wannan zaɓe matuƙar za a ba su damar shiga takarar ba tare da an yi musu ƙwange ba.

Shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Yobe, Alhaji Yakubu Shehu Damagum ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ta NNPP a Jihar Yobe ta shirya tsaf don shiga zaɓen ƙananan hukumomin matuƙar Hukumar Zaɓe ta Jihar Yobe ta amince ta sayar musu da fom ɗin tsayawa takara.

Shugaban ya ce, Jam’iyyar NNPP ba ta wata tantama a kan shiga zaɓen, kamar yadda wasu ke cewa jam’iyyun adawa a jihar ba za su shiga zaɓen ba, inda ya fito ƙarara ya ƙaryata wannan magana.

Ya ƙara da cewar, babban abin da ke gabansu shi ne samun fom ɗin tsayawa takarar daga Hukumar Zaɓen jihar da kuma samun ainihin ’yan takarar da ke da sha’awar tsayawa takarar.

Ya bayyana cewa domin kuwa ya zuwa yanzun ɗan takara ɗaya tak suka samu na kansila daga Ƙaramar Hukumar Karasuwa, wanda shi kaɗai ne ya zuwa yanzu ya fito ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a duk Jihar Yobe, amma ba su san nan gaba.

Shugaban na NNPP ya ƙara da cewar, tuni Jam’iyyarsu ta NNPP ta tura takardarsu zuwa Hukumar zaɓe ta Jihar Yobe domin bayyana shirinsu na shiga zaɓen.

Shi ma Shugaban Jam’iyyar AD, Malam Habu Doro Potiskum bayyana wa Aminiya matsayarsu a kan cewa, su ma a shirye suke su shiga cikin wannan zaɓe na ƙananan hukumomi a Jihar ta Yobe, amma kuma suna sara ne suna duba bakin gatarinsu, domin ba zai yiwu a ba su ga ana aikata ba daidai ba kuma su zuba ido, kasancewar akwai amanar al’umma a kansu.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Ya ce, suna sane da cewar kai da kaya duk mallakar wuya ne, ma’ana da Hukumar Zaɓen jihar da ma’aikatanta duk mallakin Gwamnatin Jihar Yobe ne, inda ba za su taɓa yarda ’yan takararsu a kowane mataki su faɗi zaɓe ba, wanda hakan ke nuna cewar, in jam’iyyun adawa suka shiga ma, sun san yadda sakamakon zaɓen zai kasance.

Game da ko jam’iyyarsu tana da ’yan takara, sai shugaban ya bayyana cewa, zuwa yanzu ba su da ɗan takara ko da guda, wanda a ganinsa hakan ba ya rasa nasaba da tunanin da jama’a ke yi cewar, idan mutum ya fito ma bata lokacinsa da kudinsa kawai zai yi.

Ya ce kasancewarsu ’yan jam’iyyar adawa suna ganin cewa duk wanda ya fito takara ba lallai ba ne ya ci zaɓen, komai kuwa yawan jama’arsa, domin kuwa Hukumar Zaɓe ta jihar ita za ta shirya zaɓen kamar yadda kowace jiha ke yi.

A tattaunawarsa da menema labarai kuwa da Shugaban Jam’iyyar PDM a Jihar ta Yobe dangane da yiwuwar shigar jam’iyyar zaɓen ya ce, zuwa yanzu dai kam ba su yanke shawarar komai ba a kan yiwuwar shiga zaben ko kuma akasin hakan, amma za su sanar da matsayarsu nan gaba kaɗan.

A nasa ɓangaren, Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Sanata Umar El-Gash ya ce, shakka babu jam’iyyarsu za ta shiga zaɓen kuma za a fafata da ita, fata dai kawai shi ne a yi adalci.

Continue Reading

INEC

INEC ta dakatar da wani jami’inta don gudanar da bincike kan ɓacewar takardun kaɗa ƙuri’a

Published

on

Daga Maryam Umar Abdullahi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta dakatar da wani jami’inta mai suna Mr Fred Ogboji, wanda ke kula da ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, bisa zargin ɓacewar wasu muhimman kayayyakin gudanar da zabe.

Hukumar INEC, a wata sanarwa ta ce ta dakatar da jami’in nata ne don samun sukunin gudanar da bincike a kan ɓacewar takardun kaɗa ƙuri’a na kujerar majalisar wakilai na shiyyar Bassa da Jos ta Arewa a rumfuna goma sha shida, a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Jami’a a sashen yaɗa labarai na hukumar INEC, Zainab Aminu, ta tabbatar da dakatar da jami’in, don yin bincike.

Duk da umurnin sake yin zaɓen a ranar Lahadi a wasu rumfuna, jami’an zaɓe ba su fito a kan lokaci ba, yayin da a wasu rumfunan jama’a ba su fito don sake gudanar da zaɓen ba.

KU KUMA KARANTA:Ministan Wajen Turkiyya ya yi gargaɗi  kan yiwuwar ɓarkewar rikici, saboda harin da Amurka ke kai wa ƙungiyoyin da Iran ke goyon baya

Mr. Raphael Madugu, wani ɗan jarida a jihar Filato, ya ce sun yi ta ƙoƙarin samun jami’in hukumar zaɓen don ya yi bayani kan matsalolin da aka fuskanta a rumfunan zaɓen amma bai amsa ƙira da saƙonni da aka aike masa ba.

An gudanar da zaɓen Sanata na shiyyar Arewacin jihar Filato da na majalisar wakilai na Jos ta Arewa da Bassa ne bayan da kotu ta soke waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jami’iyyar PDP, bayan da ta ce jami’iyyar ba ta da zaɓaɓɓun shugabanni a jihar Filato a lokacin da aka gudanar da zaɓukan gama gari a shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.

Continue Reading

Labarai

Zaɓen cike gurbi: Musa ya lashe kujerar Sanatan Yobe ta gabas

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Musa Mustapha a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na Sanatan Yobe ta Gabas da aka kammala.

Mataimakin shugaban jami’ar tarayya ta Gashua (FUGA), Ibrahim Ahmed Jajere, wanda shi ne jami’in zaɓe na zaɓen, ya bayyana Mustapha a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan an kammala ƙidaya ƙuri’u a cibiyar tattara ƙuri’u da ke Kwalejin gwamnatin tarayya (Federal Polytechnic Damaturu) ranar Lahadi.

Jajere ya ce ɗan takarar jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u dubu 68,778 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Aji Kolomi na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u dubu 18,878.

Jami’in zaɓen ya bayyana cewa, jimillar ƙuri’u dubu 90,949 da aka kaɗa, ƙuri’u dubu 88,771 yayin da ƙuri’u dubu 2,178 suka ɓaci.

KU KUMA KARANTA: Ɗan takarar Sanatan APC a Yobe ta gabas, ya yiwa al’ummomin Geidam da Yunusari alƙawarin morar romon dimokuraɗiyya 

“Ni, Mataimakin Farfesa Ibrahim Ahmed Jajere a nan na tabbatar da cewa ni ne Jami’in zaɓe na cike gurbi na takarar neman kujerar Sanatan Yobe ta Gabas na 2024 da aka gudanar a ranar 3 ga Fabrairu.

“An fafata tsakanin Musa Mustapha na APC ya samu ƙuri’u 68,778, Aji Kolomi na PDP ya samu ƙuri’u 18,878.

“Musa Mustapha na APC bayan ya cika dukkan sharuɗɗan doka an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya dawo zaɓaɓɓe,” in ji shi.

Mustapha wanda aka fi sani da Coolers tsohon kwamishinan kuɗi, sufuri da makamashi ne a jihar Yobe ya maye gurbin Sanata Ibrahim Geidam wanda ke riƙe da muƙamin ministan harkokin ‘yan sanda.

Ga sakamakon kamar haka;

Bursari
APC-9,466
PDP-2,752

Damaturu
APC: 11,941
PDP-6,693

Geidam
APC-6,621
PDP-2,310

Gujba
APC-11,529
PDP-3,037

Gulani
APC-12,516
PDP-2,198

Tarmuwa
APC-5,557
PDP-1,054

Yunusari
APC-11,148
PDP-834

Neptune Prime

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like