‘Yan rajin kare haƙƙin ɗan’adam a Najeriya, sun yi Alla-wadai da ƙudirin dokar da za ta hana faɗan albarkacin baki

0
52
'Yan rajin kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya, sun yi Alla-wadai da ƙudirin dokar da za ta hana faɗan albarkacin baki

‘Yan rajin kare haƙƙin ɗan’adam a Najeriya, sun yi Alla-wadai da ƙudirin dokar da za ta hana faɗan albarkacin baki

Majalisar dokokin Najeriya ta bayar da umarnin janye ƙudirin dokar da ta yi niyyar dakatar da abin da ta ƙira ayyukan zagon ƙasa a ƙasar.

Janye ƙudirin ya biyo bayan suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin jama’a da ‘yan ƙasar da ke iƙirarin cewa zai bai wa gwamnati damar murƙushe ‘yan adawa.

Kakakin Majalisar dokokin Najeriya kuma mai ɗaukar nauyin ƙudirin, Tajudeen Abbas, ya janye ƙudurin dokar a wata sanarwa a ranar Laraba.

Abbas ya ce an ɗauki matakin ne saboda damuwar da jama’a suka nuna da kuma yin la’akari da yanayin da Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Idan an tabbatar da wannan ƙudirin ta zama doka, ‘yan Najeriya na iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari ko wata babbar tara ga ɗan ƙasar da bai karanta taken ƙasa ba, da kuma hukuncin ɗaurin shekaru biyar ga masu tare hanya ba bisa ƙa’ida ba, da kafa da dokar hana fita ba bisa ƙa’ida ba ko gudanar da tattaki ba bisa ƙa’ida ba.

Masu sukar mataki kamar su Damilare Akinola ɗan rajin haƙƙin bil Adama a Abuja sun ce wani yunƙuri ne hukumomi ke yin a hana faɗar albarkacin baki

Ya ce “ƙarfin jama’a ya danne nasu, shi ya sa kake ganin an janye kudirin da ba a yi zurfin tunani ba akai. Ko kafin a fara gabatar da kudirin, an tauye hakkin jin ta bakin jama’ar Najeriya. Wannan wani yunkuri ne na kara wa hukuma karfi. Don haka, wannan yunkurin ne bai zo da mamaki ba.”

KU KUMA KARANTA:Wasu ‘yan uwa 2 a Zariya sun binne ƙaninsu da ransa

Kudirin ya tanadi duk wani dan kasa da ya bijire wa hukuma ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.

An gabatar da kudirin ne yayin ake zanga zangar kin jinin gwamnatin a Najeriya.

Tun da farkon wannan wata, dubban mutane sun yi tattaki a kan titunan manyan biranen Najeriya, suna kira ga gwamnatin ta janye sauye-sauye da ta yi musamman janye tallafin man fetur.

Sai dai zanga zangar ta koma tashin hankali yayin da jami’an tsaro suka yi amfani da karfin tuwo wurin tarwatsa masu zanga zangar. Kungiyar rajin hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce mutane 23 ne aka kashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here