‘Yan Najeriya za su fara more wutar lantarki awa 24 ba tare da ɗauke wa ba – Minista Adebayo
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce ‘yan Najeriya ba da jimawa ba za su fara more wutar lantarki ba tare da yankewa ba.
Yayin kaddamar da gine-gine a Cibiyar Koyon Harkokin Wutar Lantarki ta Najeriya (NAPTIN) a Abuja, Adelabu ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta nuna jajircewa wajen sauya alkawura zuwa aiki.
Ya ce kasar ta samu mafi girman adadin samar da wuta da isar da ita a tarihi.
KU KUMA KARANTA: An sake samun katsewar layin wutar lantarki a Najeriya
Ministan ya kara da cewa gwamnati na haskaka jami’o’i, asibitoci, cibiyoyin lafiya da al’ummomi, tare da shirye-shiryen kera na’urorin auna wuta, igiyoyi, injinan sauya wuta da batir a cikin gida.
Daraktan NAPTIN, Ahmed Nagode, ya ce ayyukan da aka kaddamar za su kara karfin cibiyar wajen horas da matasa domin kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi.

Tarayyar Turai da gwamnatin Faransa sun tallafa da kudade da fasaha ga shirin, inda Jakadan EU, Gautier Mignot, ya bayyana cewa kungiyar ta zuba fiye da Yuro miliyan 200 a bangaren wutar lantarki tun daga 2008, tare da sabon kunshin Yuro miliyan 100 da zai samar da karin megawatt 400 nan da 2027.









