‘Yan Najeriya su dinga kashe wayoyinsu daga 12 na dare zuwa 2 na rana – Ƙungiyar ƙwadago

0
18
'Yan Najeriya su dinga kashe wayoyinsu daga 12 na dare zuwa 2 na rana - Ƙungiyar ƙwadago

‘Yan Najeriya su dinga kashe wayoyinsu daga 12 na dare zuwa 2 na rana – Ƙungiyar ƙwadago

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ƙungiyar Ƙwadago ta ce Kiran zai fara aiki daga tsakar daren ranar laraba 13 ga watan Fabareru har zuwa ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2025 domin nuna adawa da karin kuɗin kiran waya da Data da Kamfanonin sadarwa sukayi da kaso 50 cikin 100.

KU KUMA KARANTA:NLC za ta gudanar da zanga-zangar gama-gari akan ƙarin kuɗin ƙira da sayen data

A wata takardar bayan taro da da Kungiyar ta NLC ta fitar mai dauke da sa hannun Shugabanta na kasa Joe Ajaero da babban sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja sunyi Allah wadarai da karya yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Kamfanonin sadarwa da NLC a tsakar daren ranar litinin data gaba ta.

Layukan wayoyin da NLC ta nemi a rika kashewa sun hada da MTN da AIRTEL da kuma GLO.

Kun shirya fara kashe wayoyin hannunku domin biyayya ga umarnin NLC?

Leave a Reply