‘Yan Najeriya na kuka da taɓarɓarewar wutar lantarki a ƙasar

0
53
'Yan Najeriya na kuka da taɓarɓarewar wutar lantarki a ƙasar

‘Yan Najeriya na kuka da taɓarɓarewar wutar lantarki a ƙasar

Kamfanin wutar lantarki ya bayyana dalilin sake rugujewar tashar wutar lantarki ta ƙasa a karo na 12.

A wata sanarwa da Babban Manajan Hulda da Jama’a na TCN, Misis Ndidi Mbah ta fitar, ta bayyana lamarin da ya faru da misalin karfe 11:29 na safe a matsayin hargitsi, wanda hakan ya sa aka yi kokarin farfado da shi cikin gaggawa wanda ya dawo da wuta a shiyar Abuja cikin dan kankanin lokaci.

Mbah ta bayyana cewa, matsalar mita ce ta haddasa katsewar wutar da aka samu a daya daga cikin tashoshin, wanda daga baya aka rufe don hana ci gaban matsalar .

Mbah ta ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan dawo da na’urorin da nufin daidaita wutar lantarki, kuma hukumar ta TCN na hasashen cewa za a iya zama cikin rashin wuta har sai an kammala gyara da inganta wutar a kasa baki daya.

KU KUMA KARANTA:An dawo da wutar lantarki a wasu yankunan arewacin Najeriya – TCN

A halin yanzu, Mbah ta ce TCN na aiki kan muhimman turakun samar da wutan, wadanda suka hada da gyaran layukan watsa wutar lantarki mai karfin 330kV da ke kan hanyar Shiroro na Jihar Neja– da Mando a Kaduna, da kokarin inganta tashar Jebba, da kuma dawo da layin watsa wuta na Ugwuaji–Apir 330kV.

Bugu da kari, bin shawarwari daga rahoton bincike da Kampanin ya gudanar game da rugujewar da ta gabata, TCN ta ce ta kara himma don magance raunin tsarin da aka gano a cikin kayan aikin babbar tashar , in ji Mbah.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya danganta rugujewar wutar lantarki ta kasa a ranar Alhamis da tabarbarewar mitoci daga 50.33Hz zuwa 51.44Hz.

A halin yanzu dai wasu sassa na birnin tarraiya Abuja na cikin duhu har yanzu.

Leave a Reply