No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan Najeriya ba za su iya jure mulkin APC sama da 2027 ba — Kwankwaso

Shugaban jam’iyyar NNPP ta ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna ƙwarin gwiwa cewa ‘yan Najeriya za su canza yanayin mulkin kama-karya da APC ke yi a 2027.

Kwankwaso ya faɗi hakan ne a yayin da ya ke karɓar mabiya jam’iyyar APC 977 na ƙaramar Hukumar Dala da su ka bar jam’iyyar zuwa NNPP a Kano a yau Alhamis a gidan sa da ke Miller Road.

A cewar Kwankwaso, gwamnatin APC ta gaza gurin cika alkawuran da ta daukar wa ƴan Nijeriya, inda ya yi kira ga ƴan ƙasa da su yi ƙoƙari su canja gwamnatin a 2017.

KU KUMA KARANTA:Kwankwaso ya ɗauki nauyin yin magani ga yaron da ke fama da ciwon yunwa a Katsina

“Talauci, yunwa, rashin tsaro da rashin aikin yi sai ƙaruwa su ke. Magidanta ba sa samu su ciyar da iyalan su.

“Wannan lokaci ne da ƴan Arewa da ma Nijeriya baki daya za su tashi tsaye su kawo canji da kan su.

“Su na ganin ba za a iya canja su ba saboda su na da tsaro da hukumar zabe, to idan guguwar canjin ta bisa su da kan su za su yi gudun famfalaƙi,” in ji Kwankwaso

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...