‘Yan mata uku sun tsere a lokacin da ake ƙoƙarin safarar su zuwa ƙasar Libya

2
382

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Osun ta tabbatar da cafke wani da ake zargi da safarar mutane mai suna Muideen Adebisi, wanda ya yi yunƙurin sace wasu ‘yan mata huɗu daga Ile-Ife a jihar Osun zuwa ƙasar Libya.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya gayyaci ‘yan matan ne zuwa wani bikin zagayowar ranar haihuwa a wani otal da ke Ile-Ife, inda ya ba su abinci da abin sha.

KU KUMA KARANTA:‘Yan sanda sun kama jami’an tsaron Rarara saboda harbin iska

Bayan da matasan suka yi barci, sai kawai suka farka a wani wuri a Kano da ake sarrafa takardu don tafiya Libya. A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, uku daga cikin matasan sun tsere inda suka tuntuɓi iyayensu bayan sun farfaɗo.

“Wanda ake zargin (Muideen Adebisi) ya gayyaci ‘yan matan zuwa bikin zagayowar ranar haihuwa a wani otel da ke Ile-Ife kuma ya ba su abinci da abin sha. Bayan barcin da matasan suka yi, sun taso ne a jihar Kano kan hanyarsu ta zuwa birnin Tripoli fadar mulkin ƙasar Libya.

Uku daga cikin matasan sun yi abin al’ajabi sun tsere a Kano inda suka kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda. Uku daga cikin matasan an sake haɗuwa da iyalansu, amma har yanzu ba a san inda matashin na huɗu yake ba,” in ji sanarwar.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, ‘yan sandan sun ce wanda ake zargin ya dage cewa ‘yan matan huɗu sun amince su tafi Libya da son rai. Ɗan’uwansa da ke zaune a birnin Tripoli ya umarce shi da ya samo ‘yan mata ya tura su wurin wani mutum a Kano wanda zai kai su Libya.

Kakaƙin ‘yan sandan ya ƙara da cewa Adebisi ya ƙara shaida wa ‘yan sanda cewa a lokacin da ya isa gidan mutumin a Kano, ya haɗu da ‘yan mata da dama da ake yi musu magani domin tafiya ƙasar Libya.

Hukumar ta PPRO ta ba da tabbacin gudanar da bincike mai zurfi sannan ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban ƙuliya nan gaba kaɗan.

2 COMMENTS

Leave a Reply