No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan majalisar wakilai 5 daga jam’iyar ‘Labour Party’ sun koma APC

‘Yan majalisar sun haɗa da Esosa Iyawe (daga jihar Edo) da Tochukwu Okere (daga Imo) da Donatus Mathew (daga Kaduna) da Bassey Akiba (daga Cross River) da Kuma Daulyop (daga Filato).

Bayan komawa zama a majalisar wakilan Najeriya a yau Alhamis, ‘yan majalisar 5 daga jam’iyyar Labour suka yi sauyin sheka zuwa jam’iyyar APC.

‘Yan majalisar sun hada da Esosa Iyawe (daga jihar Edo) da Tochukwu Okere (daga Imo) da Donatus Mathew (daga Kaduna) da Bassey Akiba (daga Cross River) da Kuma Daulyop (daga Filato).

KU KUMA KARANTA:‘Yan majalisar wakilai sun rage kashi 50 a albashin su

Har ila yau, dan majalisa Erhiatake Sueno (daga jihar Delta) da ‘yar tsohon gwamnan Deltan James Ibori sun yi sauyin sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Tsaffin ‘ya’yan jam’iyyar Labour sun kafa hujja da rabuwar kanu a cikin jam’iyyar a matsayin babban dalilinsu na yin sauyin shekar.

Bbayan shafe shekaru fiye da 20 tana gwamgwarmaya, a matsayin wani bangare na kungiyar kwadago, jam’iyyar Labour tayi nasarar shiga fagen siyasar Najeriya a zaben 2023, inda ta samu kujerun sanatoci 6 da na ‘yan majalisar wakilai fiye da 34.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...