‘Yan kasuwa a Najeriya, sun ƙalubalanci Ɗangote da BUA kan hauhawar farashin Suga

0
27
'Yan kasuwa a Najeriya, sun ƙalubalanci Ɗangote da BUA kan hauhawar farashin Suga

‘Yan kasuwa a Najeriya, sun ƙalubalanci Ɗangote da BUA kan hauhawar farashin Suga

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Ƙungiyar Ƴan kasuwa ta Kasuwar Singer, SIMDA, a jihar Kano son yi kira ga kamfanonin Dangote da BUA da su sauko da farashin suga.

Da ya ke sanyawa da manema labarai, wadanda su ka je ofishin sa domin jin bahasin farashin kayaiyakin masarufi a Kano, shugaban SIMDA, Barista Junaidu Muhammad Zakari, ya ce babu wani dalili da zai sanya farashin suga ya ci gaba da hauhawa bayan cewa a gida Nijeriya a ke yin sa.

A cewar Zakari, idan ma an yi maganar tashin farashin kuɗaɗen waje, ai farashin dala akan Naira ya sauko, “saboda haka bai kamata farashin kayan ya ci gaba da tashi ba.”

KU KUMA KARANTA:Ɗalibi ya lashe N5 miliyan a tallan siminti na Dangote

“Abun damuwa ne. Farashin sauran kayaiyakin masarufi na sauka, amma na suga ya ki sauka ko kuma ya sauka da ɗan kadan.

“Shi fa sugan nan a gida ake yin sa ba a kasar waje ba. Yayin da wasu kayan da ake yi a kasar waje ke sauka, me zai hana farashin suga da ake yi a gida sauka?

“Sabo da haka mu na kira ga kamfanonin Dangote da BUA da su daure su rage farashin suga domin al’umma su samu sauki, musamman ma da watan azumin Ramadan ke ƙaratowa,” a cewar Zakari.

Leave a Reply