‘Yan Houthi na Yaman sun ce sun kai hari kan jiragen ruwan Isra’ila da Amurka da Birtaniya 102 tun bayan ɓarkewar rikicin Gaza a watan Oktoban da ya gabata.
Shugaban kungiyar Abdul Malik al Houthi ya ce, an kai wa wasu jiragen ruwa na Isra’ila da Amurka da Birtaniya hari a cikin kwanaki 202 na hare-haren wuce gona da iri kan Gaza.
KU KUMA KARANTA: Mayaƙan Houthi sun kai wa jirgin ruwan Amurka hari a Bahar Maliya
Ya ce kusan jiragen ruwa biyu masu alaka da Isra’ila ne dakarun Houthi ke kai wa hari a kullum.
Ya kara da cewa, “Yawan zirga-zirgar jiragen ruwa na Amurka a cikin Tekun Maliya ya ragu da kashi 80 cikin 100.”