’Yan daba sun kashe abokin ango a wurin taron ɗaurin aure
’Yan daba sun kashe wani ɗan shekara 25 a wurin taron ɗaurin auren babban abokinsa a Jihar Neja.
Matashin, mai suna Murtala Hassan, wanda shi ne babban abokin ango ya gamu da ajalinsa ne a yayin da yake rabon faɗa a wurin bikin auren a unguwar Barkin-Sale da ke garin Minna.
Shaidu sun ce matashin wanda ke sana’ar ɗinki ya rasu ne bayan an soka masa wuƙa a rikicin ƙungiyoyin ’yan daba masu gaba da juna ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na dare.
Wani mazaunin unguwar Barikin-Sale ya ce, rikicin kungiyoyin an daɗe ana yin sa, ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar sun yi nasarar kashe;yan ta;adda 29
Kakakin ’yan sanda a Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa sun samu rahoton kashe matashin a lokacin da yake ƙoƙarin raba faɗan ɓata-gari.
Ya ce ’yan sanda sun je sun ɗauke gawar a wurin inda suka kama mutum guda da ake zargi, amma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin.