‘Yan Boko Haram sun kashe sama da mutane 40 a Yobe – ‘Yan sanda

0
176

Al’ummar Jihar Yobe na zaune lafiya kusan shekara ɗaya kafin wannan hari, a cewar mazaunan yankin.

A ƙalla mutane 40 aka kashe daga tsakanin ranar Litinin zuwa Talata a Jihar Yoben Nijeriya bayan da wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka harbe wasu mutanen ƙauye tare da dasa nakiya, a wani gagarumin hari na farko da aka kai jihar a cikin wata 18, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Laraba.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare agogin Nijeriyar a ranar Litinin a ƙauyen Gurokayeya da ke ƙaramar hukumar Gaidam, in ji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Abdulkarim Dungus.

Ya ce ‘yan bindigar sun buɗe wuta a kan mutanen ƙauyen, inda suka kashe aƙalla mutum 17 sai kuma a ranar Talata wata nakiya ta fashe ta hallaka mutanen ƙauyen 20 a lokacin da suke komawa gidajensu daga jana’izar mamatan da aka fara kashewan.

KU KUMA KARANTA: Boko Haram sun halaka babban limamin Masallacin juma’a a jihar Borno

Ƙungiyar Boko Haram ta sha kashe mutane da sace su a Jihar Borno, inda a can suka fi aiwatar da ayyukansu tsawon shekara 14.

Shugaba Bola Tinubu da majalisar ministocinsa sun amince da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na dala biliyan 2.8 don ayyukan gaggawa da suka haɗa da na tsaro da fannin soji.

Tinubu, wanda batun taɓarɓarewar tattalin arziƙi ya sha masa kai a yanzu, har yanzu bai ce komai ba a kan yadda zai magance matsalar rashin tsaro a wasu sassan arewacin ƙasar.

Al’ummar Jihar Yobe na zaune lafiya kusan shekara ɗaya kafin wannan hari, a cewar mazaunan yankin.

Karo na ƙarshe da bam ya tashi a Jihar Yoben shi ne a watan Afrilun 2022.

Wani mazaunin jihar Lawan Ahmed, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mayaƙan sa kan sun buɗe wuta ne kan mai uwa da wabi daga kan baburansu, inda mutum 18 suka mutu a ranar Litinin.

Leave a Reply