‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da yaran da suka dawo daga ƙasar waje a Kwara

1
430

An yi zargin cewa an yi garkuwa da wasu dangi guda uku da suka haɗa da matar da ‘ya’yan wani ɗan ƙasar waje da ya dawo gida a jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne a unguwar Okanle-Fajeromi dake ƙaramar hukumar Ifelodun, a ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

An ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar da ke kusa da Idofian inda suka yi garkuwa da mutanen a lokacin da suke kwance a gidajensu.

An ruwaito cewa matar wani mutumi mai suna Sikiru Abiola wanda ya dawo daga ƙetare kimanin shekaru uku yana aikin noma tare da ‘ya’yansa maza biyu waɗanda suka yi garkuwa da su da ƙarfi suka tafi da su.

Olugbense na Okanle wanda shi ne Bale (shugaban al’umma), Alhaji Abdulfatai Olasunkanmi ya tabbatar da faruwar lamarin.

KU KUMA KARANTA: Bayan ya yi kwanaki a hanun masu garkuwa da mutane, an sako babban limamin Ondo

Ya ce ‘yan bindigar sun isa unguwar ne da tsakar daren ranar litinin lokacin da mutanen ƙauyen suka yi barci suka shiga gidan Alhaji Sikiru suka yi awon gaba da mutanen.

Ya ce ’yan banga a garin sun amsa ƙarar da Alhaji Sikiru Abiola ya yi.

Bale ya ce “An harbe ɗaya daga cikin ‘yan banga a ƙafa a lokacin da suke fafata rikici da masu garkuwa da mutane kuma tuni aka garzaya da su asibiti.

“Amma an ceto ɗaya daga cikin ‘yan uwa da aka sace”.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwar lamarin a yau laraba.

Okasannmi ya ce, “A yau Laraba ne aka samu rahoton lamarin kuma an tura jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro domin tseratar da daji.

Okasanmi ya ƙara da cewa “Har yanzu ba a ƙubutar da mutanen da aka sace daga hannun masu garkuwa da mutane ba amma mutanen mu suna kan hanyarsu kuma muna fatan za a ceto su.”

1 COMMENT

Leave a Reply