Harbin harsashi ya jikkata ’yan sanda biyu yayin da wasu mutum bakwai ’yan gida ɗaya suka faɗa tarkon garkuwa na wasu ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Bwari da ke Abuja.
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kuma harbe wani mutum mai suna Alhaji wanda ya yi wa ’yan sandan jagora a ƙoƙarin tunkarar ’yan ta’addan da suka kawo wa iyalan hari.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan bindigar a baya bayan nan sun tsananta kai hare-hare a ƙauyukan da ke yankin Bwari, inda suke kashe na kashewa sannan sun yi garkuwa da wanda tsautsayi ya faɗa kansa.
Wani mazaunin Bwari mai suna Isaiah Samuel da ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho a wannam Juma’ar, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba yayin da ’yan bindigar suka kai farmaki kan al’ummar Zuma 1 da ke Bwarin.
KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a Bauchi sun bankaɗo bindigogin AK-47 da miliyan 4.5 a maɓoyar masu garkuwa da mutane
A cewarsa, ’yan bindigar sun yi dako wuri-wuri a ƙoƙarinsu na samun nasarar cimma buƙatarsu ta garkuwa da iyalan.
Ana tsakar haka ne waɗanda aka kawowa harin cikin sanɗa suka gaggauta ƙiran wani ɗan uwansu domin a kawo musu ɗauki.
Sai dai dan uwan wanda ya yi wa ’yan sandan jagora zuwa gidan ya gamu da ajalinsa nan take yayin da aka soma musayar wuta tsakanin ’yan ta’addan da jami’an tsaro.
Samuel ya ce a sanadiyyar musayar wutar ce ’yan sanda biyu suka jikkata, yayin da ’yan bindigar suka samu nasarar tserewa da waɗanda suka kawowa farmakin.
Kazalika, Samuel ya ce makamancin wannan hari ya auku yayin da a Talatar da ta gabata ’yan bindiga suka kai farmaki ƙauyen Barangoni da ke Bwari, inda suka jikkata wani ɗan bijilanti sannan suka yi awon gaba da wasu mutum uku.
Samuel ya yi ƙira ga jami’an tsaro da su kawo musu ɗauki a sakamakon yadda ta’adar garkuwa da mazauna yankin ta tsananta a baya bayan nan.
“Gaskiyar magana ita ce yankin Bwari yana cikin matsanancin yanayi, saboda a cikin makonni biyu da suka gabata, ’yan bindiga kawai zaraya suke suna kashewa da garkuwa da mutane,” a cewar Samuel.
Aminiya ta tuntuɓi mai magana da yawun ’yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine domin jin ƙarin bayani, inda ta nemi a ba ta lokaci ta gama tattara bayanai.