‘Yan bindiga sun yi garkuwa da babban Limami a jihar Ondo

2
299

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo ta tabbatar da yin garkuwa da Ibrahim Bodunde-Oyinlade, babban limamin ƙungiyar USO a ƙaramar hukumar Owo ta jihar.

An yi garkuwa da babban Imam mai shekaru 67 a gonarsa da ke ‘Asolo Farm Camp’ da yammacin ranar Asabar.

Wani ɗan uwa ya ce sun kai rahoto ga ‘yan sanda lokacin da Bodunde-Oyinlade bai dawo gida ba da ƙarfe biyu na rana kuma ba a amsa ƙiran wayarsa.

“Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi dangin amma har yanzu ba su nemi a biya su kuɗin fansa ba,” in ji shi da sharaɗin a sakaya sunansa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama mai bawa masu garkuwa da mutane labari a Abuja

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ’yan sanda da ’yan banga suna tseguntawa dajin suna neman babban Limamin.

Mista Odunlami-Omisanya ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa an gano motar mamacin da wayar salula a gonar.

“Da misalin ƙarfe 6 na yamma ne ‘yan uwa suka zo ofishin ‘yan sanda da ke unguwar USO.

Ya ƙara da cewa “DPO, ‘yan sanda da ƴan banga suna bincike a yankin domin samun ceto.”

2 COMMENTS

Leave a Reply