‘Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji 11 a jihar Benuwe

Wasu ‘yan bindiga a daren Lahadi sun kai hari kan wata motar fasinja ta Benuwe Link tare da yin garkuwa da aƙalla mutane 11, kamar yadda majiyoyi da dama suka bayyana a ranar Litinin.

Sai dai an ce direban motar da fasinjoji huɗu sun tsere bayan harin da aka kai da misalin ƙarfe 10 na dare a kan hanyar Ogbokolo zuwa Otukpa a ƙaramar hukumar Okpokpwu a jihar Benuwe. Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa tun farko masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su Naira miliyan 60, amma sun sauƙo zuwa Naira miliyan 16 a matsayin kuɗin fansa domin su sako fasinjojin.

Irin wannan lamarin da ya shafi motocin bas guda biyu na kamfanin sufurin ya faru ne a ranar 10 ga watan Satumba, kuma an yi garkuwa da mutane 28.

An sako mutane 26 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su yayin da biyu ke hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan sanda a Bauchi

Mista Omale Omale, Kwamishinan Wutar Lantarki, Makamashi da Sufuri ya tabbatar wa manema labarai hakan a Makurɗi. Sai dai ya ce har yanzu cikakkun bayanai na abin da ya faru na cikin zane.

A halin da ake ciki, Cibiyar Kula da Talabijin ta Najeriya ta shiyyar Makurɗi, NTA, ta ce daga cikin fasinjojin da aka sace har da ma’aikacin su.

Daraktan shiyya na cibiyar, Pam Nyam, ya sanar da ‘yan sanda faruwar lamarin, ya kuma buƙaci ɗaukar matakin gaggawa don ceto dukkan fasinjojin da aka sace.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *