’Yan bindiga sun sako jaririya da mata 2 a Abuja

’Yan bindiga sun sako jaririya da matan aure biyu daga cikin mutanen da suka sace a unguwar Arab road da ke yankin Kubwa a Abuja.

’Yan bindigar sun shiga yankin ne da misalin karfe 8 na daren Lahadi, suka yi awon gaba da wata mata da ’ya’yanta huɗu da kuma ’yar aikin gida.

Kazalika sun yi awon gaba da wata matar aure da ke unguwar.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka sako, Zainab Hassan, ta ce tana zaune a wani gininsu da ba a kammala ba, sai ta hangi ana dukan mijin ta.

Ta ce, “Na tunkare su ne don na ji abin da ke faruwa, a lokacin ne suka ture shi gefe suka umarce ni na bi su.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun sace mutum 7 a Abuja

“Sun kai mu maɓoyarsu da ke cikin daji kafin su sauya shawara suka sako ni da jaririyar makwabcina ’yar watanni shida da wata mata.”

Wani jami’in tsaro a yankin, Abubakar Adam, ya ce wasu mazauna yankin tare da jami’an tsaro sun yi yunkurin tunkarar maharan lokacin da suke barin yankin.

“Amma dole ta sa muka fasa tunkararsu duba da cewar ba mu da wasu makamai na kirki da za mu iya wani abun,” in ji shi.

Wasu mazauna yankin, waɗanda suka zanta da Aminiya sun bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da aka kai hari a yankin cikin watan nan na Disamba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *