’Yan bindiga sun kai hari inda suka sace dalibai da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi (CUSTECH).
A daren Alhamis ne ’yan bindigar suka kutsa harabar jami’ar da ke yankin Osara, inda suka ɗauke ɗalibai da kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Wani ɗalibin jami’ar wanda ya tsallake rijiya da baya, mai suna John, ya shaida mana cewa “Misalin karfe 9 na dare muka fara jin ƙarar harbi a lokacin da muke cikin ɗakunan karatu saboda muna shirye-shiryen jarabawa.
“Wasunmu sun tsere, amma na san an kama wasu ɗalibai”, in ji wani ɗalibin jami’ar mai suna John.
KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a jihar Delta
Rahotanni daga jami’ar sun ce ’yan banga da ke yankin sun kai ɗauki, amma maharan sun fi su ƙarfin makamai.
Zuwa wannan lokaci dai babu cikakken bayani saboda mahukunta sun ƙi cewa komai a kai, sai nan gaba.
Mun tuntuɓi kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, amma har muka kammala rubuta wannan labarin ba mu ji daga gare shi ba.